ABUBUBWA GUDA HUDU SUNA RAGE IMANI

1-Rashin Tadabburi acikin ayoyin Allah na shari'a dana Kauniyya.

wato mutum baya karanta Alqurani ko kokarin sanin ma'anarsa ko dubi abisa abina yake koyarwa,da kuma rashin tunani acikin halittun Allah,sai hakan ya sanya bawa ya manta da Allah ya daina jin tsoransa, hakan shine babban hasara da raguwar imani.

2-Kauda kai daga sanin sunayin Allah da siffofinsa wannan yana kara nisanta bawa daga sanin Allah da jin tsoransa da azuciya sai hakan ya sanya masa raguwar ayyuka da rashin kwadayin rahamar Allah, wanda hakan shine babban hanyar raguwar imani.

2-Karancin ayyukan ibada,hakika duk lokacin da bawa yake karanta ayyukan da'a haakan yana nuna raguwar Imaani da jin tsoran Allah.

4-Yawaita Sabon Allah,duk lokacin da mutum yake yawan sabon Allah kuma baya tuba,to wannan yana raguwar imani da jin tsoran Allah a zuciyarsa.

Allah ka kayi mana kariya daga raguwar Imani.

1
$
User's avatar
@Usainiusa posted 3 years ago

Comments

Ameen ya Allah

$ 0.00
3 years ago