1. Duk kwan lantarki ko kyandir a tabbatar an kashe su, kada a kunna sai daidai lokacin da ake bukatar haske.

  2. Indomie tana da sauki da kuma rahusa. Amma a kiyaye gishirin dake cikinta, domin yana da illa.

  3. A rika amfani da mizani ko sikeli wajen tantance abincin da za a dafa a gida. Hakan zai rage barna da kuma tabbatar abun da aka dafa daidai yake da bukata.

  4. Ba dole ba ne a ci abinci sau 3 a kowacce rana, idan har babu yunwa ko sau biyu 2 kawai aka ci abinci babu laifi.

  5. Gero, dawa da masara suna bukatar hidima sosai kafin su zama abinci. A guje su dukka, sai dai idan babu wani zabin.

  6. Danwake yana da nagarta wajen kashe yunwa, kuma ba ya bukatar hidima sosai.

  7. Dumame yana da albarka. Idan abinci yayi saura a tanada shi domin da safe a yi dumame.

  8. Idan akwai beraye a gida a tabbatar an halaka su da guba mai karfi. Baraye suna yin barnar kayan abinci da kuma sacewa.

  9. Idan har kana da wayar salula baka bukatar agogo; idan kana da agogo ka sayar a sayo wani abu mai amfani.

  10. A dakatar da yin sabuwar sutura, na dan wani lokaci, sai dai idan ya zama dole.

  11. Wajen girki amfani da gawayi yafi sauki.

  12. Idan maigida ya je kasuwa ya tarar farashin kayan abinci ya karu, koda kadan ne, to a sanar da uwargida, domin ita ma ta san halin da ake ciki. Haka zai taimaka wajen tsumin abinda ake da shi da kuma kyautata tattalin arzikin iyali.

1
$
User's avatar
@Khaleepha posted 3 years ago

Comments

Nura. Check

$ 0.00
3 years ago