NI MA TSINTOWA NAYI. 😂

  1. Idan wuri ba shi da nisa, to a daure a taka a kafa. in hakan zai kara lafiyar jiki da kuma kiyaye ‘yan kudade.

  2. Akwai kayan abinci masu kosarwa da basu bukatar a dora su a wuta; kamar garin kwaki da sukari, da ‘yar gyada mai gishiri. Idan a inda kake akwai gurasa ita ma zata kashe yunwa ba tare da an kashe kudade da yawa ba.

  3. A rage yin baki da kuma kai ziyara har sai idan ya zama dole. A karfafa zumunci ta wayar salula.

  4. Idan za a dafa shinkafa a jika ta sosai, kafin a dora ta a wuta. Sannan yayin da take kan wuta a sa ido sosai.

  5. A guji barnar kudi wajen sayen naman miya. Amfani da wake ko ganye kamar alayyaho yafi rahusa da kuma kara lafiyar jiki.

  6. A rika dora zogale, ko tafasa a abinci suna hanzarta koshi da kara lafiya.

1
$
User's avatar
@Khaleepha posted 3 years ago

Comments