why we create content in Hausa language,Hausa language, the most important indigenous language in West and Central Africa, spoken as a first or second language by about 40–50 million people.
Mafi yawan mutane suna ganin Wi-Fi a wayarsu, amma wasu basu san amfaninsa ba. Wasu ma sai su kunna shi, su barshi kawai a haka.
MENENE WI-FI?
Wi-Fi fasaha ce ta hanyar sadarwa, wadda ba ta amfani da waya. Tana baiwa na’urori irin su kwamfutoci na hanu (Laptops) da kwamfutar tebur (Desktop). Sannan tana baiwa wayoyin hannu (wayoyi irinsu iPhone, Android), da sauran kayan aiki (madaba’o’i da Kyamarorin Bidiyo) su yi mu’amala da Intanet. Wi-fi tana ba da dama a wadannan na’urori, da wasu da dama don musayar bayanai tare da juna, da kirkirar hanyar sadarwa. Wi-Fi tana bada dama kai tsaye ga amfani da Intanet a wadannan abubuwan da muka lissafo.
Wi-Fi ba lakabi bane; suna ne na kamfani wanda kamfanin kasuwanci ya kirkira wanda ake nufin ya zama matsayin hatimin hulda da juna don kokarin yada kasuwancin ta hanyar Intanet.
Ana ganin Wi-Fi ne a kusa da inda mutum yake kunna ‘data’ dinsa idan zai yi mu’amala da Intanet (browsing).
Yanzu kamfanonin masu gyara waya sun kai makura wurin fiddo da waya masu saukaka al’amuran yau da gobe. Wayoyi masu WiFi ko kuma a rubuta wlan wato ‘wireless’ za su iya browsing ba tare da layi a cikin wayarsu ba kuma ba tare da ka saka modem a kwamfutarka ba, kuma za ka yi komai da komai da ita wanda ya shafi Intanet.
Shi Wi-Fi (wireless) ba zuwa ake a sauke shi daga ‘play store’ ba, a’a wayar ce take zuwa dashi. Domin dole sai akwai ‘wireless card’ ko ic a jikin na’urar me wireless.
YAYA AKE KUNNA WI-FI HAR A BA WA SAURAN WAYOYI KO KWAMFUTOCI?
Ka tabbatar akwai ‘wireless coberage’ a kusa da kai. Kamar irinsu Jami’a, manyan kamfani, café’s, shoping mall, plaza, da sauran wurare wadanda kan iya saka wireless router. Jama’a suna iya kama wa, su yi amfani dashi a kyauta.
Idan ka samu irin wadannan wurare da akwai Wireless din, sai ka kunna WiFi din wayarka. Idan kana kokwanton akwai wireless din ko babu, to kawai ka kunna WiFi din wayarka, ita za ta fada maka idan akwai wireless din ko babu. Za ka ga ta kama ‘abailable wireless’ sannan ta fada maka ko ‘open’ ce ko kuma ‘wep/shared key’ aka saka mata.
Idan ‘open’ ce, za ka iya ‘connecting’ ba tare da ka sa ka ‘password’ ba, sai ka yi ‘browsing’ a kyauta.
Wani amfanin WiFi shi ne, idan kana cikin ‘browsing’ sai data dinka ya kare, za ka iya cewa abokinka ya kunna WiFi (Hotspot) dinsa, sai ka yi ‘connecting’ ta hanyar hotspot, sai ka ci gaba da ‘browsing’ dinka. Yadda ake yi shi ne, idan za ka bude WiFi dinka, domin abokinka ya kama, to da farko za ka kunna data dinka.
Idan ka kunna data din, sai ka je ‘setting’ na kan wayarka, idan ka taba setting, zai nuno maka ‘Network & Internet’ sai ka taba shi. Shi kuma zai budo maka WiFi a farko, sai shi ma ka taba shi, za ka ga ‘Hotspot & Tethering’ sai ka taba shi, zai nuno maka ‘WiFi Hotspot’. Idan ka taba ‘WiFi Hotspot’ zai nuno maka Off, zai ka mayar dashi On, wato ka kunna shi kenan.
A can kasa za ka ga ‘Hotspot password’ idan kana so sai ka saka password, idan kuma baka bukata, sai ka barshi haka. To ka bada dama a abokinka ya kama wayarka, ya yi browsing da data din wayarka. Ko da waya, ko kuma da Kwamfuta.
Shi kuma wanda zai kama din, idan da Kwamfuta ne, a fuskar Kwamfutar, can kasa, ta bangaren dama, zai ga alama kamar haka ‘//////’ sai ka taba shi, za ka ga yana ‘searching’ to zai kamo wayar, sai ka saka password ka ci gaba da browsing kawai.
Idan kuma da waya za ka kama, to sai ka shiga ‘Settings’ ka bude ‘Network &Internet’ sai ka bude WiFi da ‘WiFi Direct’ shikenan za ka ga ya fara ‘searching’ zai kamo maka wayar, sai ka yi browsing dinka da data din abokinka.
Atakaice amfanin WiFi shi ne, ka yi browsing da data din wani, a wayarka, ko a kwamfutar ka.