Tsokaci A Kan Fasahar 5G Da Ayyukanta

0 17
Avatar for techhausa
2 years ago
Topics: Technology

why we create content in Hausa language,Hausa language, the most important indigenous language in West and Central Africa, spoken as a first or second language by about 40–50 million people.

Kafin mu shiga batu a kan Fasahar 5G kai-tsaye, ya kamata mu fara da takaitaccen bayani a kan shi ‘G’ din, wato (GENERATION). Muna da 1G, 2G, 3G, 4G yanzu kuma ga 5G ta bayyana. Sauri ko rashin sauri na abubuwan da muke yi a kafar sadarwa duk ya ta’allaka ne a kansu.  Sannan kowanne a cikinsu masana ne suka zauna na tsawon shekaru domin samar da shi.

1G, wanda ake nufin “First Generation of cellular network” an samar da shi ne a shekarar 1979 wato lokacin da aka fara samar da wayar salula kenan. Fasahar ta ba da damar kiran waya ne kadai (boice call). Sannan kuma wayoyin da suke amfani da shi, wato irinsu Motorola da sauransu ba su da batiri mai rike caji, kuma ita kanta sadarwar ba ta da cikakken tsaro. Iya tsananin saurin 1G shi ne 2.4Kb/s. Hakan ya sa masana shiga bincike gadan-gadan domin kirkiro fasahar da tafi 1G, wato 2G.

A shekarar 1991, masana sun sami nasarar kirkiro fasahar 2G, wanda a lokacin ne wayoyin salula suka sami damar yin sababbin ayyuka da ya wuce kiran waya kawai. 2G ta samar da cikakken tsaro a wayoyin sadarwa na wancan lokacin. Sannan ya kara saurin sadarwa daga 2.4Kb/s zuwa 1Mb/s. Fasahar ta ba da damar tura sakonnin SMS, MMS, da kuma hada wayoyi sama da guda biyu a lokacin kira (conference call). Kafin daga baya a samar da fasahar 3G.

An samu nasar kirkiro fasahar 3G ne a shekarar 2001. Wanda ya kawo manyan sauye-sauye a duniyar sadarwar wayar salula, kamar shiga yanar-gizo (web browsing). Ka ga kenan fasahar 3G ce ta ba da damar kirkiro manhajoji irin su Facebook, YouTube, Google da sauransu. Sannan fasahar 3G ce ta ba da damar tura sakonnin E-mail, sauke bideo a kan Intanet (bideo downloading), tura hotuna (picture sharing) da sauransu. Sannan wannan fasahar kamar sauran ta kara saurin sadarwa daga 1Mb/s zuwa 2Mb/s.

Abu dai yana ta ci gaba, sai aka sake samar da fasahar 4G, wadda aka kirkire ta a shekarar 2009. Fasahar 4G ta kawo canji mai girman gaske a duniyar sadarwa, musamman ta bangaren sauri daga 2Mb/s zuwa 1Gb/s. Hakan ya ba da damar samun sadarwa mafi inganci da tsaro. Ita ce fasahar da ta kawo sada mutane da yawa a bidiyo (bideo conference). Duk wasannin (online games) da ‘boice message’ da muke yi duk fasaharce ta kawo su. Fasahar 4G ita ce wadda muke amfani da ita a yanzu.

Ana cikin haka sai kuma ga fasahar 5G ta danno kai a shekarar 2020, wanda take da tsananin saurin da har ana tunanin za ta iya taba lafiyar dan’adam. Saurin 5G ya ninka na 4G sau talatin da biyar (×35). Kamar yadda na yi bayani 4G na da makurar saurin tafiyar 1Gb/s, to shi 5G yana tafiya ne da saurin 35.46Gb/s, wanda ba a taba samun irin wannan tazarar a tarihi ba. Har yanzu ana takaddama a kan cutarwa ko rashin cutarwarsa. Saboda wasu masana na ganin ‘medium’ din da ke daukan ‘signal’ din wato ‘radio wabe’ baya iya shiga jikin dan’adam, wasu kuma na ganin zai iya shiga. Yanzu haka akwai wayoyi da dama masu amfani da 5G kamarsu GALAXY S21 ULTRA da GALAXY S20.

To ita fasahar 5G ci gaban harkar sadarwa ce wato network, a baya ana amfani da wasu wayoyi ne da ake kira ‘dial of connection’ da ake latsa su kafin a samu damar hawa intanet.

Daga baya kuma aka fara samun ci gaban network irin ‘gprs’, sai aka samu ‘edge’, sannan aka samu 3G da 4G kamar yadda na yi bayani a baya. Kowace fasaha ta fi wadda ta gabace ta sauri, ma’ana ana samun ci gaba kenan da bunkasa fasahar sadarwar.

Kamfanin Huawei da ZTE na kasar China ne suka fara fitowa da sabuwar fasahar ta 5G. Amma a baya, kamfanonin sadarwa na kasar Amurka ne ke kirkirar fasahar 2G, 3G da sauransu.

Hakan kuma na nufin kamfanin na Huawei zai samu riba sosai idan mutane suka fara amfani da fasahar.

Haka kuma a bangaren wurin sauke bidiyo ko kallonsa a intanet wato streaming, idan 5G ne za a samu matukar sauri ta yadda misali, idan mutum yana iya sauke bidiyon 2GB ko 3GB cikin awanni ko mintuna 30 zuwa 40, a fasahar 5G ba zai wuce minti 10 ko 5.

Fasahar 5G ba tana nufin farashin ‘Data’ zai canza ba ne, cikin ‘data’ da mai amfani ke siya dai za a cire daidai abin da ya yi amfani a bar masa sauran.

Ba wai an kirkiro ‘5G network’ ba ne domin amfanin wayoyin hannu kawai, babban dalilin kirkiro wannan fasahar domin samun sauki a kayayyakin da ake dorawa a intanet ne, wato a takaice fasahar ‘Interner of Things’ (IoT) da kuma uwa uba ‘kuantum computers’ wanda ita ce dukkan alamu na wannan zamani na fannin fasaha ya nuna cewa za ta zama 6th generation na computer.

A shekarar 1991, masana sun sami nasarar kirkiro fasahar 2G, wanda a lokacin ne wayoyin salula suka sami damar yin sababbin ayyuka da ya wuce kiran waya kawai. 2G ta samar da cikakken tsaro a wayoyin sadarwa na wancan lokacin. Sannan ya kara saurin sadarwa daga 2.4Kb/s zuwa 1Mb/s. Fasahar ta ba da damar tura sakonnin SMS, MMS, da kuma hada wayoyi sama da guda biyu a lokacin kira (conference call). Kafin daga baya a samar da fasahar 3G.

An samu nasar kirkiro fasahar 3G ne a shekarar 2001. Wanda ya kawo manyan sauye-sauye a duniyar sadarwar wayar salula, kamar shiga yanar-gizo (web browsing). Ka ga kenan fasahar 3G ce ta ba da damar kirkiro manhajoji irin su Facebook, YouTube, Google da sauransu. Sannan fasahar 3G ce ta ba da damar tura sakonnin E-mail, sauke bideo a kan Intanet (bideo downloading), tura hotuna (picture sharing) da sauransu. Sannan wannan fasahar kamar sauran ta kara saurin sadarwa daga 1Mb/s zuwa 2Mb/s.

Abu dai yana ta ci gaba, sai aka sake samar da fasahar 4G, wadda aka kirkire ta a shekarar 2009. Fasahar 4G ta kawo canji mai girman gaske a duniyar sadarwa, musamman ta bangaren sauri daga 2Mb/s zuwa 1Gb/s. Hakan ya ba da damar samun sadarwa mafi inganci da tsaro. Ita ce fasahar da ta kawo sada mutane da yawa a bidiyo (bideo conference). Duk wasannin (online games) da ‘boice message’ da muke yi duk fasaharce ta kawo su. Fasahar 4G ita ce wadda muke amfani da ita a yanzu.

Ana cikin haka sai kuma ga fasahar 5G ta danno kai a shekarar 2020, wanda take da tsananin saurin da har ana tunanin za ta iya taba lafiyar dan’adam. Saurin 5G ya ninka na 4G sau talatin da biyar (×35). Kamar yadda na yi bayani 4G na da makurar saurin tafiyar 1Gb/s, to shi 5G yana tafiya ne da saurin 35.46Gb/s, wanda ba a taba samun irin wannan tazarar a tarihi ba. Har yanzu ana takaddama a kan cutarwa ko rashin cutarwarsa. Saboda wasu masana na ganin ‘medium’ din da ke daukan ‘signal’ din wato ‘radio wabe’ baya iya shiga jikin dan’adam, wasu kuma na ganin zai iya shiga. Yanzu haka akwai wayoyi da dama masu amfani da 5G kamarsu GALADY S21 ULTRA da GALADY S20.

To ita fasahar 5G ci gaban harkar sadarwa ce wato network, a baya ana amfani da wasu wayoyi ne da ake kira ‘dial of connection’ da ake latsa su kafin a samu damar hawa intanet.

Daga baya kuma aka fara samun ci gaban network irin ‘gprs’, sai aka samu ‘edge’, sannan aka samu 3G da 4G kamar yadda na yi bayani a baya. Kowace fasaha ta fi wadda ta gabace ta sauri, ma’ana ana samun ci gaba kenan da bunkasa fasahar sadarwar.

Kamfanin Huawei da ZTE na kasar China ne suka fara fitowa da sabuwar fasahar ta 5G. Amma a baya, kamfanonin sadarwa na kasar Amurka ne ke kirkirar fasahar 2G, 3G da sauransu.

Hakan kuma na nufin kamfanin na Huawei zai samu riba sosai idan mutane suka fara amfani da fasahar.

Haka kuma a bangaren wurin sauke bidiyo ko kallonsa a intanet wato streaming, idan 5G ne za a samu matukar sauri ta yadda misali, idan mutum yana iya sauke bidiyon 2GB ko 3GB cikin awanni ko mintuna 30 zuwa 40, a fasahar 5G ba zai wuce minti 10 ko 5.

Fasahar 5G ba tana nufin farashin ‘Data’ zai canza ba ne, cikin ‘data’ da mai amfani ke siya dai za a cire daidai abin da ya yi amfani a bar masa sauran.

Ba wai an kirkiro ‘5G network’ ba ne domin amfanin wayoyin hannu kawai, babban dalilin kirkiro wannan fasahar domin samun sauki a kayayyakin da ake dorawa a intanet ne, wato a takaice fasahar ‘Interner of Things’ (IoT) da kuma uwa uba ‘kuantum computers’ wanda ita ce dukkan alamu na wannan zamani na fannin fasaha ya nuna cewa za ta zama 6th generation na computer.

1
$ 0.00
Avatar for techhausa
2 years ago
Topics: Technology

Comments