Mindset(Tunani)

0 10
Avatar for techhausa
2 years ago
Topics: MIND SET, read.cash

why we create content in Hausa language,Hausa language, the most important indigenous language in West and Central Africa, spoken as a first or second language by about 40–50 million people.

Tunani da zai chanja akalar zuciyarka, ita kuma zuciya ta chanja akalar jikinka, shi kuma jiki ya chanja akalar yanayinka, shi kuma yanayi ya chanja akalar rayuwarka, ita kuma rayuwa ta fitar da sakamakon aikinka. Wannan tunanin shi ake kira da MIND SET.

Duk abinda kaga mutum ya zama a rayuwarsa sakamakon tunaninsa ne, kenan idan kana so ka chanja rayuwarka sai ka chanja tunaninka.

YADDA ABIN YAKE.

Idan ka shuka mangwaro a gonarka tabbas mangwaro ce zata fito.

TUNANI shine IRI (SEED) da ka SHUKA - ZUCIYA itace GONARKA - MANGWARO itace abinda ka zama a RAYUWARKA.

Haka idan ka shuka tunani mai kyau sakamakon tunanin ne zai fito a rayuwarka.

Idan kaga LEMO akan bishiya to tabbas idan ka tona karkashin bishiyar zaka ga jijiyar lemon ce ta samar da bishiyar. Duk abinda ka gani a WAJE sakamakon abinda ke CIKI ne. Abinda dan adam ya aikata sakamakon tunaninsa ne.

Dukkanin abinda Mutum ya zama ko zai zama a duniya yana karkashin abubuwa uku ne, idan suka hadu sai su bada sakamakon yadda ya zama. Abubuwa sune:

1)T=THINKING ma'ana tunani

2)F= FEELING ma'ana jin abu a zuciya.

3)A=ACTION ma'ana aikin da mutum ya aikata.

Idan suka hadu sai abinda Mutum ya zama, abinda Mutum ya zama shi ake kira sakamako wato R=RESULT.

Idan muka takaice abin zai bamu ( T=F=A=R)

Tunanin da ka ke yi yana sanyawa kaji abin a zuciyarki, jin abin a zuciya yana kai ka zuwa aikata abin, aikata abin yana kaika zuwa ga sakamako aikin.

Idan ka yi TUNANI (THINKING) kana Bukatar Kudi=>sai KAJI (FEELING) ka fara son Kudin a Ranka ==>sai kaji kana neman AIKI (ACTION) da zaka yi ==>sai kaga ka samu KUDI (RESULT) . Kaga ashe sai da ka fara tunanin kudi wannan tunanin shine ya kaika ga hanyar da ka samu kudin.

Dangote ya zama dangote ne saboda da tunani da yake yi a zuciyarsa. Inda kaima zaka yi tunani irin na DANGOTE da tabbass zaka zama DANGOTE. BUHARI ya zam SHUGABAN KASA ne sabada TUNANINSA da zaka iya irin tunanin da BUHARI yake yi da zaka zama Buhari.

DOMIN KA FAHIMTA DA KYAU.

MANZON ALLAH SAW yace: "a cikin jiki akwai wata tsoka idan ta baci dukkanin jiki ya baci inda ta gyaru dukkan jiki ya gyaru, tsokar itace zuciya" Manzon Allah yayi maganar Ilimi wanda akan wannan zan iya rubuta littafi mai PAGES 1000 ban gama bayanin salon kimiyyar da manzon Allah yake nufi ba. Yawanci rashin zurfafa tunani yasa muka bar ilimi da yawa. Manzon Allah yana da fasahar magana wanda mu sai mun zurfafa ilimi kafin mu fito da zahirin maganar.

A takaice manzon Allah yana nufin zuciyar mutum itace gangar jikinsa, shi kuma gangar jiki shine rayuwarsa. Abinda yasa manzon Allah yace ZUCIYA, saboda itace ke tunani kuma itane ke jin so, zafi, farin ciki da sauran su.

ALLAH YACE : "Idan da zaku yi TAWAKKALI da ya Azurta ku kamar yadda yake azurta tsuntsu"

Malamai da yawa sun takaita ilimi akan wannan ayar, akwai bukatar fadaɗa ilimi sosai domin fahimtar balaga da ilimin dake cikin wannan ayar. Bincikena ya nuna mini duk wani tattalin arziki na cikin wannan ayar.

Allah yace inda zaku TAWAKKALI, maye tawakkali? Tawakkali na nufin FEELING (wato sanyawa arai) da ya azurtaku kamar yadda yake azurta tsuntsu (kenan tsuntsu shi tawakkali yake shi yasa Allah ya azurta shi)

RARRABEWA.

idan mukayi TAWAKKALI Allah zai azurta mu, kenan idan muna son arziki abinda muke bukata shine TAWAKKALI. Tawakkali ko ya kunshi abubuwa uku wanda yake daidai da tsarin da na bayar :

Tunani, Imani, aiki wanda ya yi daidai da (T--F--A) wato (THINKING, FEELING, ACTION) Idan mukayi Tawakkalin zamu samu arziki, yayi daidai da ragowar 'R' wato RESULT. Gaba daya ayar ta kunshi T=F=A=R.

JARABAWA.

Kaima mai karatu yanzu ka fara tunanin mai kake son zama a rayuwarka, da zaran kayi tunanin zaka ji kana son zama abin, zaka ji kana aikata duk abinda zai kaika ka zama abin watarana sai kaga ka cika burinka.

Kayi amfani da wannan tsarin na T=F=A=R rayuwarka zata chanja sosai.

1
$ 0.00
Avatar for techhausa
2 years ago
Topics: MIND SET, read.cash

Comments