Duk da takura da barazanar gobnati akan abunda ya shafi crypto hakan bai saka yan Nigeria sunja baya ba wajen amfani da cypto, sai ma kara shiga cikin harka da sukayi tsundum inda a yanzu zaiyi yuwa ka samu matashin da baya mu’amala da crypto a Nigeria.
"why we create content in Hausa language,Hausa language, the most important indigenous language in West and Central Africa, spoken as a first or second language by about 40–50 million people."
Shiyasa ba zo mana da mamaki ba a lokacin da bincike ya nuna cewa.Najeriya ita ce kasa ta 6 a jerin kasashen duniya wajen karbar kudin cryptocurrency, lamarin da ke nuni da tsayin daka na tsarin hada-hadar kudi tsakanin ‘yan kasa tun bayan da babban bankin Najeriya ya haramta amfani da kudin cryptocurrency.
Bayan da babban bankin Nigeria sukayi doka akan amfani da kudin internet na crypto,nan ne kuma matasa da dama suka tashi haikan wajen cin moriyan harkan na crypto inda suka rika amfani da tsarin P2P suna cigaba da yin crypto.
P2P tsarin da ke bada daman ka saya kudin internet daga abokin huldar ka ya taimaka sosai musamman wa yan Nigeria wajen saukake musu hanyar sayan kudin internet a daidai lokacin da ya zama bankunan kasan sun hana su amfani da tsari katin banki wajen sayan crypto tsarin P2P ya taimaka matuka.
A yanzu da alumman Nigeria suka karbi Crypto hannu biyu zamu iya cewa babban abunda suke bukata shine sanin ilimin da zai taimaka musu wajen cigaba da yin aiki da crypto, an samu masana da dama da suke bude wuraren koyar da karatun crypto akwai kuma manyan kamfanoni da suke kokari a yanzu wajen ganin sun bada gudumawa sosai a harkan crypto a Nigeria irin BItcoincash Nigeria.
Bitcoincash Nigeria suna kokari sosai wajen kirkirar bidio da kuma rubuce rubuce masu yawa da harshen turanci dama hausa don ganin sun taimakawa alumman Nigeria sun fahimci harkan crypto yanda ya kamata, a wannan kokarin nasu har sun bude katafare ofishi a yanzu haka a cikin garin Yola na jihar Adamawa wato BCH HUB wanda shine irin shi na farko a arewa suna kuma shafukan sada zumunta harma da shafin Youtube https://www.youtube.com/channel/UCEAW3cYj4I4sDx0pm0Nm6pA
Alama dai yana nuna nan da yan wasu shekaru masu zuwa Nigeria zata iya yin fintinkau a harkan hada hadar kudin internet Crypto.