Bitcoin Cash Explain in Hausa

0 23
Avatar for techhausa
2 years ago

Bitcoin cash kudin internet ne na musamman wanda yasha bambam da sauran kudin internet da ake dasu.

Ta hanyar saurin mu’amala,saukin chaji,Hanyoyin amfani dashi da kuma community na musamman da bitcoin cash ke dashi wanda babu wani kudin internet dake da irin shi, wannan dalilan yasa bitcoin cash yayi fice.

Saukin mu’amala da kuma saurin biyan bukata na daya daga cikin dalilan da ya saka muke amfani da kudin internet ,bitcoin cash ya rufe kofa a wannan fannin domin zamun iya cewa a yanzu babu wani kudin internet daya kai bitcoin cash saurin transaction,cikin giftawan ido kana tura bitcoin cash daga wallet naka zuwa ga abokin huldan ka zai gani anan take.ba tare da bata lokaci ba.

Nawa za’a chajemu ma’ana transaction fees shine abu na farko da muke dubawa a duk lokacin da zamu tura kudin internet,daga cikin kudin internet da ake dasu akwai wanda in zaka tura dala goma za’a chaje ka dala hamsin koh fiye da hakan,a bitcoin cash ba haka tsarin yake ba domin koh nawa zaka tura a bitcoin cash chajin bai kai ya kawo ba.

Ana iya amfani da bitcoin cash wajen saya da sayar wa akwai shaguna da dama da suke karban bitcoin cash, zaka iya ziyartan map.bitcoinscash don ganin shagunan dake karban kudin internet na bitcoin cash a kusa dakai.


2
$ 0.00
Avatar for techhausa
2 years ago

Comments