```✔ Kasa farin ciki a zuciyar Maraya yafi ka kwana kana Sallah
✔ Kuyi gaggawar aikata alheri karkuce sai kunyi kudi mai yawa
✔A Kyautata niyya idan za'ayi aikin alheri domin asamu yardar Allah.
✔ Ayi hankali da Riya, domin tana shiga cikin aikin mutum ta barauniyar hanya.
✔ Sadaqah tana janyo maka samun nasara tare da taimakon Ubangiji acikin dukkan abinda kasa agabanka.
✔ Sadaqah tana sanyawa ka samu gagarumar nasara akan Maqiyanka da mahassadanka. Kuma kaidinsu ba zai cuceka ba.
✔ Idan wani ciwo yana damunka har ka rasa maganinsa, to yawaita sadaqah. In sha Allah ita Sadaqah magani ce, waraka ce, kuma kariya ce daga dukkan cututtuka.
✔ Sadaqah ladanta yana tabbatuwa awajen Allah. Koda dabbobi kayi wa sadaqar, ko tsuntsaye, ko Kwari.
✔ Sadaqah garkuwa ce daga sharrin 'barayi, ko gobara, kuma tana kiyaye masu yinta daga mummunar cikawa.
✔ Babbar sadaqar da zaka fara gabatarwa ayanzu, ita ce kayi "sharing" (wato ya'da) wannan rubutun daga Zauren Fiqhu ba tare da goge koda harafi guda daga ciki ba.
Idan kayi haka da niyyar sadaqah, to duk wanda ya gani ya karanta kaima kana da lada akansa.```
little bit good idea