Menene Bitcoin?

1 28
Avatar for nurain
Written by
2 years ago

Bitcoin wani tsarin kudi ne da ake amfani da shi a intanet kadai, kuma yana amfani a duk duniya ta hanya bai daya, kuma babu wani banki guda daya da yake kula da wannan nau’in kudin, wani masanin fasaha mai suna Satoshi Nakamoto ne ya kirkiro fasahar Bitcoin a shekarar 2009, kuma masu ta’ammuli da nau’in kudin sun a yi a tsakanin su ba tare da wani mutum na uku ba wanda zai lura da ta’ammulin tsarin sakar sama na intanet ne kawai ke kulla ta’ammulin.

Ana yin amfani da kudin Bitcoin wajen musanyar kudade a sahar intanet, ana iya siyan hajoji ma, a shekarar 2015 kadai ‘yan kasuwa kimanin 100,000 ne suka yi mu’amala da kudin Bitcoin, ana iya amfani da kudin na Bitcoin domin zuba hannun jari a wasu kamfanoni, a wani bincike da jami’ar Cambridge ta gudanar a shekarar 2017 ta gano akwai akalla kusan mutum sama da miliyan biyar da suke amfani da kudin na Bitcoin.

Ta Ya Ya Wannan Na’uin Kudin Yake Aiki?

Wannan it ace tambayar da kowa yake yi in ya ji maganar wannan nau’in kudin, kamar dai yadda wadanda su ka san yadda ake kulla cinikayya ta sahar intanet, mutum zai siya abunda yake so sai ya biya ta akant din sa a shagonnan da su ke sahar intanet (Online Stores) to haka shima Bitcoin Cash ake cinikayya da shi akwai shagonnan sahar intanet har ma da shagunan da ba a yanar Gizo suke ba a kasuwannin mu yanzu Zaka samu shaguna da dama suna karban Bitcoin Cash BCH suke yarda da cinikayya da nau’in kudin na Bitcoin, ta yadda mutum in ya ga abun da ya ke sha’awar siya a shagonann sahar intanet da suke karbar nau’in kudin sai kawai ya shiga bayanen jikar ajiyar kudin shi na Bitcoin (Wallets) a take shagon sahar intanet za su cire kudin su daidai da cinikayyar da ya yi.

Domin mallakan Bitcoin wallet zai Ka ziyarci wannan adreshin https://www.bitcoin.com/

Koh kuma wannan adreshin na playstore https://play.google.com/store/apps/details?id=com.bitcoin.mwallet

Daga nan zaka fara Amfani kaima da Bitcoin Cash BCH wajen saye da sayarwa.

BCH Nigeria

7
$ 0.01
$ 0.01 from @Strange1
Avatar for nurain
Written by
2 years ago

Comments

WOW,I never knew you were an hausa man,nice article tho but it sad I don't understand the language. We continue to promote BCH

$ 0.00
1 year ago