Yadda Zaka Gane Site Na Karya Dakuma Na Gaskiya

0 28
Avatar for UmarFarouq
3 years ago

Assalamu alaikum, ina fatan kowa da kowa Yana cikin koshin lafiya.

Yau zamuyi bayanine akan wani Abu Mai matukar muhimmanci duba da yadda ake ta samu karuwar Al amarin, wannan kuwa shine; yadda zamuyi gane site na karya dakuma na gaskiya

  • Hanya ta farko dai shine kayi laakari da Wanda ya turo maka da duk wani link kafin kashiga, domin mutane kala kala ne, a kwai masu copy and paste akwai kuma wadanda sai sun tabbatar da Abu kafin su yada

  • Hanya ta biyu kuma shine, laakari da abinda link din ya kunsa. Misali, zaa turo maka link ace kayi register zaka samu $500 kyauta 🤣🤣 wannan kawai rainin wayone kokuma ace kashiga kayi reg. Amma dole sai kasa password dinka na gaskiya, to wadannan kuma so suke su kwace maka account 🙄😲

  • Sai kuma Abu na karshe Wanda shine mai MATUKAR MUIMMANCI; a duk lokacin da kashiga kowanne shafi na yanar gizo ka tabbata cewa ka duba URL/Search bar domin tabbatar da cewa site na gaskiya kake assessing. A dan lokacinnan ansami wani rumous da yake yawo a kafar whatsApp dangane da NPOWER, idan kuka lura zakuga cewa address din da suka bayar shine: 👉👉 https://npower-fmhds-gov-ng.we.app ❌❌, Amma ainihin site din NPOWER na na gaskiya shine: 👉👉https://npower.fmhds.gov.ng ✔️✔️. Saboda haka ka tabbatar duk site din daka shiga kaduba saman browser ka domin tabbatar da sahihancin site din da ka shiga

Ina gdy dafatan kuma zakuyimin comments dayawa dakuma likes

6
$ 0.00
Avatar for UmarFarouq
3 years ago

Comments