Nigeria kafin samun Yancin kai

1 228
Avatar for Sunusi91
4 years ago

NIGERIA KAFIN SAMUN YANCIN KAI

Daga shafin Lili Kafinga

An samu kafuwar kasar Najeriya ne sanadiyar hadakar wasu tsofafffin dauloli da suka rayu a matsayin kasashe mabambanta masu zaman kansu shekaru aru-aru kafin zuwan Turawan mulkin mallaka. Gabanin shigowar Turawan mulkin mallaka, mutanen kasar nan na zaman lafiya da juna tare da yin harkar kasuwanci ba tare da kokawar neman samun arzikin kasa ko mulki ba, a dukkan sassan kasar. Kowane bangare yana amfani da tsarin mulkinsa na asali domin tafiyar da harkokin shugabantar al'ummar sa. Wannan ya kawo cigaban yankunan kasashen.

Kafin samun 'yancin kai, Turawan kasar Potugal su ne suka fara shigowa Najeriya don harkar kasuwanci ta tashar ruwan Lagos da na Calabar a karni na 17 zuwa na 19. Turawan yayin shigowar su suna musanyar kayayyakin masarufi da bayi a wancan lokaci, kuma shugabannin al’ummar wuraren ne kadai ke mu’amala da su kuma ke samun riba daga cinikin da ke gudanar.

A shekarar 1807 ne kasar Birtaniya ta dakatar da cinikin bayi a Najeriya bayan yake-yake da wasu kasashe. Bayan wasu lokuta kasar Birtaniya ta kafa wata rundunar soja a Afirka ta Yamma a wani yunkuri na dakatar da cinikin bayi da kasashen duniya ke yi. A shekarun 1884 zuwa 1885 ne aka gudanar da wani babban taro a kasar Jamus, taron da aka kira shi da suna "Berlin Conference," inda aka kakkasa kasashen Afirka zuwa yankuna daban-daban na mulkin mallakan Turawa. Bayan taron, Birtaniya ta samu yankuna da dama a Yammacin Afirka, kuma Najeriya na daya daga cikin kason da aka ba ta. Har zuwa wancan lokacin ikon Turawan mulkin mallakar bai karasa Arewacin Najeriya ba, yawancin ikonsu ya tsaya a yankin kudanci da yammacin kasar.

A shekarar 1903 Turawan sun sami nasarar mamaye Arewa bayan tafka gumurzu tsakaninsu da dakarun sarakunan Daular Usmaniyya, wannan ne ya yi sanadiyyar rasuwar marigayi Sarkin Musulmi Attahiru da faduwar Daular Sokoto. Turawan mulkin mallakar sun cafke sarakuna kamar Sarkin Kano bayan ya ki mika musu wuya, inda suka kulle shi a yankin Lokoja. Bayan wannan ne Turawan suka sami mallakar yankunan biyu da yankin Lagos.

A shekarar 1914 ne wakilin Sarauniyar Ingila a kasar Gwamna Janar Fredrick Lugard ya hade yankunan Kudu, Yamma da Arewa aka sa wa kasar suna Najeriya. Yadda Najeriya ta sami sunanta Najeriya ya samo asali ne daga kogin Niger inda a ranar 8 ga watan Janairun shekarar 1897, wata ’yar jarida wadda daga baya Fredrick Lugard ya aura, mai suna Dame Flora Louisa Shaw, ta rubuta wata kasida a jaridar "The Times" ta Ingila, cewa ya kamata a sa wa kasar Najeriya suna Najeriya wato “Niger da Area”, saboda kogin Niger da ya rasa ta cikin kasar.

2
$ 0.00
Avatar for Sunusi91
4 years ago

Comments