Hausa, in Nigeria

1 21

*KADDARA TA RIGA FATA.... 21*

15-02-1442 / 03-10-2020

*LITTAFIN PROF. MANSUR IBRAHIM SOKOTO.*

*YADAWA A SOCIAL MEDIA,*

*MUHAMMAD IBRAHIM*

*KHALIFANCIN UMAR DAN KHADDABI (R. A).... 5*

*YADDA UMAR YAKE KULA DA DUKIYAR JAMA'A*

Umar ya kasance mai yawan tsentseni dangane da dukiyar al'umma da yake kula da ita a matsayinsa na shugaban Musulmi. Kuma ya kan tsananta ma kansa da iyalansa dangane da ita. Ga wasu daga cikin labaran irin taka tsantsan da yake yi:

1. Umar ya kan kashe fitilar gwamnati idan ya kare aikinda ya shafi jama'a sannan ya kunna tasa domin kada ya shiga hakkin da ba nasa ba.

2. A lokacin da yaronsa ya ba shi madara ya sha yana tsammanin daga rakumarsa ne, amma daga baya ya gane daga rakumar gwamnati ne sai da ya shawarci surukinsa Sayyiduna Ali a kan wannan, Ali ya nuna masa ba kome.

3. Ya samu labarin dansa ya kiwata raqumarsa a cikin rakuman gwamnati, sai ya hane shi kuma ya umurce shi da ya mayar da abin da ta haifa a cikin taskar gwamnatin tun da yake da abincin gwamnati aka yi kiwonta.

4. Matarsa Ummu Kulsum diyar Sayyiduna Ali ta aika da kyautar turare zuwa ga matar sarkin Ruma ta hannun Manzon da ya aika masa. Da aka zo mata da tukuici sai ya umurce ta da ta mayar da shi cikin dukiyar gwamnati tun da yake Manzon da ya kai sakon gwamnati ce ta aike shi. Da ta kai kara wurin mahaifinta, Ali ya goyi bayan khalifa Umar, sai dai ya ba da shawarar a cire mata daidai abin da ta aike da shi.

5. Ya kan hana matansa su yi amfani da abin da ya rage idan aka raba Turare ko Mai ko ire irensa ko da kuwa su shafa kansu da abinda ya saura a hannayensu ne domin yana ganin ba halaliyarsu ba ne.

*YADDA UMAR YAKE NADA GWAMNONI*

Babban abin da Umar yake kula da shi a wajen nada shugaba shi ne kwarewarsa a irin aikin da ake bukata. Da yawa Umar ya kan nada mutum a kan wani mukami ya bar wasu wadanda sun fi shi daraja saboda la'akari da iyawarsa ga wannan aiki fiye da su. Ya kan gwada mutum lokaci mai tsawo kafin ya ba shi mukami kamar yadda ya tsayar da Ahnafu dan Kaisu tsawon shekara guda a Madina, sannan ya ce masa, na jarabta ka na lura da alheri a zahirinka, kuma ina fatar badininka ya kasance haka. Sannan ya yi masa wa'azi, ya nada shi gwamna.

Wani abin da zai bayyana mana ma'aunin da Umar ke gane wanda ya cancanci mukami da shi, shi ne, labarin yadda ya nada Shuraihu a matsayin alkali. Ga yadda labarin ya ke:

Watarana halifa Umar ya dauki hayar doki daga wani talaka, ya kuma yi masa sharadin cewa, su biyu ne zasu hau dokin da shi da wani amininsa. Ga alama wannan dokin bai yi kwarin da zai dauki dawainiyar Umar tare da abokinsa ba. Amma duk da haka wannan bawan Allah ya amince, watakila don ganin Sarkin Musulmi zai yi amfani da shi. Kuma ko ba komai idan dokin ya samu matsala Umar mai iya ranka masa ne. To, amma hasashen wannan bawan Allah sai bai zamo dai dai ba, domin kuwa a lokacin da dokin ya kasa Umar ya umurce shi ne da ya hakura ya dauki kayansa. Amma sai shi kuma ya ce bai yarda ba sai an bashi diyyar raunana masa abin hawa da aka yi. Da suka kasa cimma yarjejeniya sai Sarkin Musulmi Umar ya neme shi da ya samar da wanda zai yi hukunci a tsakaninsu. A nan ne wannan bawan Allah ya ba shi sunan Shuraihu, wanda ya ke ba sahabi ba ne amma yana daga cikin malamai masu basira. Shuraihu kuwa bayan da ya gudanar da bincike kan masalar sai ya yi hukunci da cewa, dole ne Sarkin Musulmi ya biya talakka 6arnar da ya yi masa. Dubin irin kwararan matakan da Shuraihu ya dauka na bincike da yadda ya yi karfin halin ba Sarkin Musulmi rashin gaskiya su suka sa nan take Umar ya nada shi alkali. Sai Shuraihu ya kasance shi ne nadadden alkali na farko a tarihin musulunci.

Umar ya kan shawarci mutane game da wanda za a ba mukami. Kuma a zamaninsa duk gwamnan da aka nada sai an ba shi rubutacciyar takarda da sa hannun Sarkin Musulmi a kanta wadda kuma ta kunshi sharuddan wannan aiki da aka dora masa. Ya kan halartar da jama'a don su yi shaida kamar irin tsarin rantsarwar da ake yi a gaban jama'a a wannan zamani.

A koda yaushe Umar ya kan za6ar ma mutane shugaba daga cikinsu. Ba ya dora bakauye a kan 'yan birni saboda rashin dacewar yanayinsu da al'adunsu da tunaninsu. Ya kan za6i masu ilmi don sukarantar da jama'a. Tausayi shi ma sharadi ne kafin mutum ya cancanci shugabanci a zamaninsa. Don haka, ya fasa nada wani mutum daga kabilar Banu Sulaim a kan ya ce shi bai ta6a sunbantar 'ya'yansa ba, Umar ya ce, ba ka da jinkai ke nan, ba za mu shugabantar da kai a kan jama'a ba.

Umar ya hana duk gwamnoninsa yin kasuwanci ko wane iri don gudun su nemi wani sassauci ko a yi musu rangwame don la'akari da mukaminsu sai raini ko jin nauyi ya shiga tsakaninsu da talakawansu, abin da zai iya hana zartar da adalci a wajen hukunci. A kai a kai kuma ya kan rubuta wasiku na fadakarwa da jan kunne zuwa gare su don su zamo masu amana da gaskiya da yin adalci a cikin aikinsu.

*TSAKANIN UMAR DA GWAMNONINSA*

Ana iya cewa, dukkanin gwamnoni a zamanin khalifancin Umar sun yi tasiri da tsarin tafiyar da al'amurransa. Mafi yawansu sun kasance masu tsentseni da gudun duniya kamarsa. Amma kuma duk da haka, Umar sai ya lisafta abin da gwamnansa ya tara na arziki idan lokacin karewar aikinsa ya zo. Kuma da yawa wadanda ya kar6e rabin dukiyarsu ya mayar a taskar hukuma saboda wasu dalilai da suka shafi tara kudi ta wata hanya ba albashi ba, kamar kasuwanci ko kiyo da sauransu.

Sarkin Musulmi Umar ya umurci duk gwamnoninsa da su rinka zuwa aikin hajji tare da jama'arsu domin su samu halatar taron shekara shekara da yake yi da su inda yake yi ma su gargadi a game da talakawansu. Ya kan ce da su, "Ban dora ku a kan talakawa ba don kuci dukiyarsu ko mutuncinsu ko ku zubar da jininsu. Na tura ku ne don ku tsayar ma su da Sallah, ku sanar da su addini, kuyi masu rabo a kan adalci." Ya kan sanar da talakawa cewa, suna da ikon kawo kara idan gwamnoninsu suka cuta masu.

A 6angaren gwamnoninsa da sauran sarakuna kuma, Umar ba ya yarda a wulakanta su. Don haka, duk talakkan da ya kuskura ya ci mutuncin basarakensa ko ya yi masa raini wanda bai dace ba to, Umar ba ya sassauta masa.

*ZA MU CI GABA IN SHAA ALLAH.*

2
$ 0.00

Comments

That good of you Mr, just like what you guys are

$ 0.00
4 years ago