Join 96,117 users already on read.cash

Sabon Tsarin rarara maula ce ko rainin hankali???

8 20
Avatar for Amsad17
Written by   58
1 year ago

Nayi Matukar Mamaki Da Shiga Wani Tunani Tun Lokacin Da Na Saurari Hirar Da Akayi Da Tsageran Mawakin Nan Marar Kunya, Wanda Ya Gama Zage Dukkan Manyan Mu Na Arewa Masu Mutunci, Wato Dauda Kahutu Rarara.

Inda Ya Bayyana Cewa Bazai Sake Yiwa Shugaba Buhari Waka Ba Har Sai Masoyan Buhari Sun Hada Masa Kudin Waka, Daga Naira Dubu Daya #1000. Inda Yace Akwai Wakar Da Zaiyi A Nan Gaba Amma Dai Masoya Buhari Ne Zasu Tura Masa Kudi Inda Har Ya Bayar Da Lambar Akawun (Account Number) Wanda Talakawa Zasu Tura Masa Kudin A Ciki.

Toh Ni Abinda Na Kasa Ganewa Game Da Wannan Shiri Shi Ne, Shin Wai MAULA CE Ya Dauko Ta Wani Sabon Salo Ko Kuwa Dai RAININ HANKALI NE Na Wadanda Ya Dauka Sakarkari Basu San Abinda Suke Ba?

In Banda Wannan Mutumin Ya Raina Mutane Ana Cikin Halin Da Kowa Yasan Wannan Shugaban Da Gwamnatin Sa Sun Gaza, Talaka Da Mai Kudi Kowa Da Inda Ake Wahalar Dashi. Amma Saboda Rashin Kunya Wai Ka Kawo Wani Tsari Saboda Ka Raina Mutane Kana Neman Kudi Saboda Shugaban Da Ya Kasa Taimakon Al'ummar Sa.

Toh Kalubale Ga Masu Tura Wannan Kudin Da Kuma Wadanda Suke Shirin Turawa. Wallahi Kuji Tsoron Allah! Ku Kauracewa Wannan Tsarin Domin Bazai Haifar Maku Da 'Da Mai Ido Ba.

Dalili Kuwa Bata Yiyuwa Ku Tarawa Wani Kato Makudan Kudade Saboda Ya Dauke Ku Wadanda Basu San Abinda Suke Ba. Ai Kowa Ya Sani Cewa RARARA Dan Jihar Katsina Ne, Kuma Akwai 'Yan Gudun Hijira Daga Bangarori Da Dama Na Jihar Katsina, Wanda Har Da Bangaren Karamar Hukumar Sa.

Shin Kunji Inda Ya Fito Ya Nemawa Wadannan 'Yan Gudun Hijirar Taimako Ga Al'ummar Kasar Mu Najeriya? Ko Kuwa Kunji Inda Shi Yakai Masu Nashi Taimakon Saboda Halin Da Suke Ciki?

Wato Sai Kawai Ya Kawo Wani Tsari Wanda Za Ku Kara Masa Karfi Alhalin Ga Masu Bukatar Taimako Can Wurare Daban~Daban.

Toh Wallahi Duk Talakan Da Ya Tura Wannan Dubu Dayar Munafuki Ne Wanda Babu Tausayin Dan Uwan Sa Talaka A Zuciyar Sa. Idan Kuma Masu Kudin Mu Ne Suka Tura Allah

10
$ 0.00
Avatar for Amsad17
Written by   58
1 year ago
Enjoyed this article?  Earn Bitcoin Cash by sharing it! Explain
...and you will also help the author collect more tips.

Comments

Barawon banza da wofi

$ 0.00
1 year ago

Hmm only Nigerians can relate

$ 0.00
1 year ago

Good

$ 0.00
1 year ago

Good

$ 0.00
1 year ago

Hmmmmm god forbid

$ 0.00
1 year ago

Rain in way one kawai

$ 0.00
1 year ago

Allah yakyauta

$ 0.00
1 year ago

Rabuda Dan Iska

$ 0.00
1 year ago