Nasiha a Takaice:
✍ Mansur Ibrahim Sokoto
Jinkayin Allah:
Sarkin Musulmi Umar dan Khattabu _radhiyallahu anhu_ ya ce: "Wani ayari ya zo wajen Manzon Allah _sallallahu alaihi wasallam_ sai suka tarar da wata mata daga cikin fursunonin yaki tana tatse nononta (saboda ya cika har yana damun ta), tana yawon a tsakanin fursunoni mata, duk ta samu yaro karami sai ta shayar da shi. Ana haka sai ta ga wani jinjiri (danta kenan); sai ta jawo shi da karfi ta manne shi ga cikin ta (saboda shaukin haduwa da shi da gano shi da ta yi bayan ya bace mata) sannan ta ba shi nono. Sai Manzon Allah _sallallahu alaihi wasallam_ ya ce: "Kuna ganin wannan matar za ta iya jefa dan nan nata a wuta?" Suka ce, lallai kam ba dai in tana da ikon hana shi shiga wutar ba. Sai Manzon Allah ya ce: "Hakika, Allah ya fi tausayin bayinsa fiye da tausayin wannan matar ga danta". 📚Sahihul Bukhari 5999
good indeed thus is great