Muhammadu Buhari: PDP ta ce gwamnatin APC ta jawo ƙunci da talauci

3 228
Avatar for AbubakarAdamu
3 years ago

Babbar jamiyyar hamayya a Najeriya wato PDP ta yi zargin cewa da gangan gwamnatin Shugaba Muhamadu Buhari ta ƙara farashin man fetur da wutar lantarki domin ta ƙuntata wa alumma.

A wannan makon ne kamfanin mai da hukumar wutar lantarki suka sanar da ƙarin farashin. Sai dai jam`iyyar APC ta musanta, ta na cewa PDP ce silar matsalolin ƙasar.

PDP ta yi zargin cewa ƙeta ce tsagwaro a zuciyar jamiyyar APC mai mulki, kuma wannan ne ya sa ta ninka farashin man fetur da na wutar lantarki ba tare da laakari da irin mawuyacin halin da `yan Najeriya suka samu kansu a ciki ba.

Jam'iyyar hamayyar ta ce ko farfaɗowa ƙasar ba ta yi ba daga bugun da annobar korona ta yi ma ta.

Nuna mana aikin da ka yi wa arewacin Najeriya - 'Yan Twitter ga Buhari

Gwamnatin Buhari bulunbituwa ta ke yi - Masu sharhi

Sakataren yaɗa labaran jam`iyyar mista Kola Olagbondiyan ya shaida cewa bukatar su ita ce a gaggauta soke ƙarin farashin da aka yi, don kauce wa jefa ƙasa cikin rikici.

Ya ce: `Jamiyyar mu na da yaƙinin cewa ƙarin farashin litar mai da aka yi, daga naira 87 a zamanin mulkin PDP a shekara 2015 zuwa naira 151 farashin dappo da wata manufa aka yi, sannan bugu-da-ƙari aka kara farashin kudin kilohat guda na wutar lantarki daga naira 30 zuwa naira 62.

''Jamiyyar APC ta kau da dukkan shakku cewa tana aniyar gana wa yan Najeriya azaba, don cimma wata manufarta ta son zuciya.''

Jamiyyar PDP ta ce duk mai lissafi ya san dangantakar da ke tsakanin rayuwar alumma da wutar lantarki da man fetur, don haka duk lokacin da farashinsu ya hau, to babu makawa sai talakawa sun galabaita. Kenan babu gwamnatin da ke tausayin jama`a da za ta kau da kai ga irin wannan hauhawar farashin!

Ganin cewa mai ba wata tsada can yake yi a kasuwar duniya ba, jam`iyyar PDP ta ce ba ta san da wane mizani gwamnatin Najeriyar ta yi amfani da shi wajen kara farashin man ba, saboda haka ya kamata ta fito ta yi bayani.

Martanin APC

Jamiyyar APC a nata martanin, ta ce jamiyyar PDP ba ta da bakin magana, saboda a zamanin mulkinta ne ta ba da kafar tabka almundahana a harkar mai, lamarin da ya haddasa taɓarbarewar al`amura a Najeriya.

Barrister Ahmed jamii ne a kwamitin riko na kasa na jamiyyar APC da ke shaida wa BBC cewa: Janye tallafi da PDP suka kasa yi wanda ake ɓarnatarwa suka janye.

"Kuma yanayin firashin mai a kasuwar duniya dole ya zo da irin wadanan matsaloli, amma gwamnati na hada basira da alkaluma don ganin talaka ya samu sauki.

"Sannan wayanda ke korafin kan wutan lantarki gyara aka yi ma'ana wayanda suka fi shan wuta ne su zai fi tsada kan talaka da wutar ba sosai suke samu ba."

Dangane da zargin cewa da nufi APC ke jefa alumma cikin ƙunci kuwa, Barrister Ismail Ahmed cewa ya yi, "Jam'iyyar APC da shugaban kasa Buhari duk babu wanda ke jindadin halin da ake ciki".

Barrister Ahmed ya kuma ce "ba wai don ƙeta ko cin zali hakan ke faruwa ba, kawai yanayi ne aka shiga kuma muna kokarin ganin yadda za a daidaita hakan".

Thank you Buhari: 'Yan Najeriya na yi wa shugaban kasarsu godiyar shaguɓe

Karin Bayani

Matsalar tsadar rayuwa a Najeriya ita ce damuwar mafi yawan `yan kasar, inda suke cewa ba su ga alamar gwamnati ta san irin kwakwar da suke ci ba.

Sannan suna ganin da wuya su yi saurin fahinta ko karbar uzurin gwamnati a wannan yanayi da aka yi ƙarin farashin mai da wutar lantarkin a daidai lokacin suke kokarin ta da komaɗar ƙarnin korona.

'Yan Najeriya da dama dai na ta faman yanke kauna kan cika alkawuran da gwamnatin shugaba Buharin ta sha yi musu.

Ko a kafafen sada zumunta musamman Twitter, mutane na amfani da maudu'in #BuhariHasFailed, wato Buhari ya gaza, domin nuna takaicinsu kan matsanacin halin da suke zargi ya jefa su a ciki.

4
$ 0.00
Avatar for AbubakarAdamu
3 years ago

Comments

wannan haka yake

$ 0.00
3 years ago

Koya ya karanta yayimin kwamen da like kana ya yimin subscribe

$ 0.00
3 years ago

APC is the

$ 0.00
3 years ago