Dalilai uku da Fadar Buhari ta bayar kan tsadar abinci a Najeriya

6 230
Avatar for AbubakarAdamu
4 years ago

shugaban Najeriya ta yi karin haske kan abin da take ganin ya jawo yanayin tsadar rayuwa da tashin farashi da 'yan kasar ke ta korafi a kai.

A wata hirarsa da BBC Hausa, mai bai wa shugaban kasar shawara kan harokin yada labarai Malam Garba Shehu ya ce abu uku ne suka jawo halin tsadar kayayyaki da ake fuskanta amma batun rufe iyakokin kasar ba ya daga cikinsu.

A ranar Laraba ne 'yan Najeriya da dama suka taso Shugaban ƙasar Muhammadu Buhari a gaba, inda suke ta sukarsa sakamakon tsadar rayuwa a ƙasar.

Ƙarin da aka yi na farashin wutar lantarki da man fetur na daga cikin abubuwan da suka harzuka wasu 'yan ƙasar suke sukar shugaban inda har wasu 'yan arewacin ƙasar ke ƙalubalantar shugaban kan cewa ya nuna musu aikin da ya yi musu a tsawon mulkinsa.

Sai dai a ranar Alhamis, shugaban ya bayyana damuwa kan tsadar kayayyakin abinci da ƴan kasar ke kokawa da gwamnatinsa.

Har ma Shugaba Buharin ya ce gwamnatinsa ta damu kan tsadar kayayyakin a daidai lokacin da kullen korona ya ƙara jefa tattalin arzikin ƙasar cikin wani hali, a wata sanarwa Malam Garba ya fitar.

Me ke haifar da tsadar shinkafa a Najeriya?

Nuna mana aikin da ka yi wa arewacin Najeriya – 'Yan Twitter ga Buhari

Wadanne dalilai gwamnatin Buhari ta bayar?

Malam Garba Shehu ya zayyana wa BBC dalilai uku da suka sa 'yan Najeriya suka samu kansu a hali na tsadar rayuwa kamar haka;

1. Batun taki: Karayar tattalin arziki da annobar cutar korona ta jawo wa kasashe na nesa da kusa ya shafi shifo da ma'adinai da ake amfani da su wajen sarrafa taki.

Hakan ya sa taki ya yi tsada a noman rani har zuwa yanzu, ta yadda wadansu sun noma shinkafa sun rasa takin saka mata dole ta sa suka saida wa makiyaya shinkafar. An yi haka a kasar nan.

2. Mugunta tsakanin mutane: Akwai 'yan kasashen waje da ake gani suna yi. Sayen abinci ake yi ana boye shi a kasar nan.

Kuma gwamnati na nan na daukar mataki kan wannan.

3. Kafa masana'antun shinkafa: An samu ci gaba wajen kafa masana'antun sarrafa shinkafa da yawa a kasar nan. Kamar a Kano akwai wajen 18 wanda kowanne a ciki yana sarrafa shinkafa daga tan 180 zuwa 400 a kowace rana. Suna daukar ma'aikaci bai gaza 200 ba.

Amma yanzu kowa so yake ya ga cewa masana'antarsa ba ta tsaya ba. Kasuwa ake shiga suna zuba kudi ko nawa ne ba ruwansu don su ci gaba da sarrafa masana'antunsu biya suke a ba su shinkafa danya.

Rashin gamsuwa

Sai dai duk da haka, damuwa da Shugaba Buharin ya bayyana kan tsadar kayayyakin abinci da ƴan kasar ke kokawa da gwamnatinsa, wasu 'yan ƙasar ba su gamsu ba, inda suka kafe kan cewa bai damu da halin da suke ciki ba.

Da yawa sun bazama shafin tuwita ne don baje kolin korafinsu.

Wannan mai suna Mustapha Bello ya bayyana cewa bai yarda cewa shugaban ya damu da 'yan Najeriya ba, inda ya ce sun bi layi sun zaɓi shugaban kuma sun yi wa shugaban uzurin da ba su taɓa yi wa wani shugaba ba, amma ga abin da zai saka musu da shi.

Sai dai a sanarwar da Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce wannan matsalar da Najeriya take ciki ta shafi duniya ce baki ɗaya kuma gwamnatin Buhari ta fara bin matakan shawo kan matsalar.

Daga cikin hanyoyin shawo kan wannan matsala, shugaban ya bayar da umarnin fitar da abinci kusan ton 30,000 na masara ga masu samar da abincin dabbobi domin sauƙake farashi.

Ya ce yanayin da aka shiga zai zo ya wuce.

Sai dai a shafin na Tuwita, Sulaiman Bajoga cewa ya yi mutane sun fi buƙatar wannan masara fiye da kaji domin mutane na cikin wani hali, in ji shi.

Masu ganin kokarin shugaban

Ga kuma ra'ayoyin wasu masu ganin kokarin shugaban:

Shi kuma wannan ya bayyana cewa Buhari yana ƙoƙari matuƙa a mulkinsa inda ya ke ba 'yan ƙasar haƙuri.

Wannan kuma cewa yake yi shugaban ya taimaka wa talaka ta hanyar sauke farashin abinci da samar da tsaro da kuma kula da lafiyarsa.

2
$ 0.00
Avatar for AbubakarAdamu
4 years ago

Comments

Nigeria

$ 0.00
4 years ago

A yi kokari a yimin commen da subscribe kana da kuma like

$ 0.00
4 years ago

Adai duba

$ 0.00
4 years ago

Madallah Dan goruba

$ 0.00
4 years ago

shugaban Najeriya ta yi karin haske kan abin da take ganin ya jawo yanayin tsadar rayuwa da tashin farashi da 'yan kasar ke ta korafi a kai.

$ 0.00
4 years ago

Nigeria is my country

$ 0.00
4 years ago